Majalisa Ta Amince Wa Buhari Ya Ciyo Sabon Bashin $5.8bn

Majalisar Dattijai a ranar Laraba ta sahalewa Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari ya ciyo sabon bashin Dalar Amurka biliyan 5.8.

Bashin dai na daga cikin tsarin wadanda za a ciyo na tsakanin shekarar 2018 zuwa 2020.

Amincewar dai ta biyo bayan yin nazari kan rahoton Kwamitin Basussuka na Cikin Gida da Ketare na Majalisar.

Shugaban Kwamitin, Sanata Clifford Ordia, yayin da yake gabatar da rahoton, ya ce  za a karbo $2,300,000,000 ne daga Bankin Duniya, sai wata $2,300,000,000 din daga kasar Jamus da kuma $90,000,000 daga Bankin Musulunci.

Sauran sun hada da 786,382,967 da za a karbo daga Bankin Shige da Fice na China da kuma $50,000,000 daga Asusun Bunkasa Noma na Duniya.

Sanata Clifford ya ce a ranar shida ga watan Mayun 2021 ne Shugaba Buhari ya nemi amincewar Majalisar don ta duba, sannan ta amince masa ya ciyo bashin.

A cewarsa, tsarin ciyo bashin ya ya kunshi neman karbo $36,837,281,256 daga ketare.

Ya kuma ce kwamitinsa ya mika wa Majalisar rahotonsa a watan Yulin 2021 yana neman a amince da karbo $8,575,526,537.


Follow Hausadrop On Facebook

Leave a Reply

Your email address will not be published.

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

Back to top button