Babu Abun Da Shugaban Ƙasa Baya Yi Wajan Kawo Ƙarshen Matsalar Tsaro A Nigeria

Daga: Fahad Kabir Maitata

Duk wani abun na makami da sauran kayan aiki da aka cewa shugaban kasa Muhammadu Buhari ana so ko za’ayi amfani da shi wajan magamce matsalar tsaro take yake bayarwa.

Har jiragen yaki daga kasar Amurka aka siyo domin yin aiki dasu a Nigeria.

Mataimaki na musamman ga shugaban kasa Muhammadu Buhari kan kafafen sadarwa na zamani Bashir Ahamd shine ya bayyana hakan yayin wata fira da sashin bbc a ranar Lahadi.

Bashir ya ce “Babu wani abun da shugaban kasa ba ya yi wajan ganin an kawo matsalo karshe a Nigeria”

Kazalika “ba’a taba zuwa taron majalissar tsaro ko ta kolin a Nigeria an nemi wani abu shugaban kasa ya ce ah’ah ba”

Ya kara da cewa matsalar tsoro tana da fadi sosai, kuma idan ka toshe nan gobe canne zai sake budewa, dan haka akwai bukatar al’umma su hada hannu da karfe wajan ganin am magamace ta.

Daga karshe ya ce kwarai ya kamata kowa ya fito kafar yada labarai ya nuna rashin jin dadin sa koda ran mutum 1 aka rasa, amma al’umma su sani duk wata matsala da ka gani ya kamata ace kasanarwa da jami’an tsaro tun daga unguwannin ku.


Follow Hausadrop On Facebook

Leave a Reply

Your email address will not be published.

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

Back to top button