Wasu Dalilan Da Zasu Iya Sa Mace Ta Fasa Aurenka

Za a masoya sunyiwa juna alkawarin aure, amma can daga bisani sai aga macen ta sauya ra’ayi ta fasa auren.

Hakan yasa maza dayawa suke zargin mata da yaudara, wanda a zahiri abun ba haka yake ba.

Akasarin idan irin wannan ya faru da za a yi bincike sosai za a fahimci shi namiji shine da laifi.

Ga wasu dalilai dake jawo mace tace ta fasa auren namiji koda kuwa ya kai kudi gidansu.

  • Mata masu natsuwa suna duba namijin da zasu aura wani irin namiji ne shi.

Ma’ana wajen tsari da burin da yake da shi a rayuwa.

Daga lokacinda mace ta gano kai namiji ne wanda baida buri ko bai san ciwon kansa ba. Daga wannan lokacin zata sauya tunanin ta gareka.

Mace tana son ganin namiji mai buri da kokarin neman na kansa ba dogaro da wani ko wasu ba. Don haka mace na iya fasa aurenka idan ta gano kai cima zaune ne.

  • Idan mace ta gaji da jiran namiji akan maganar aure tana iya fasa aurensa koda kuwa batada wanda zata aura.

Ita mace tana son a lokacinda ka furta mata zancen aure ya kasance a shirye kake. Idan Kuma ka nemi uzurin akaishi zuwa wani lokaci duk zata amince. Amma daga lokacinda ta fahimci bakada magana daya tana iya fasa aurenka.

Kada kayiwa mace alkawarin aure bakada tabbas akan lokacin yin auren. Domin ita mace duk yadda take ba Kai kadaine ke sonta ba. Mace mai manema a kullum tana cikin barazanar shedan ne na rabuwa da wanda take so ta kama wanda ya fishi.

Don haka ka guji jawa wacce kayiwa alkawarin aure rai ba tare da dalilai masu karfi ba.

  • Daga lokacinda mace ta fahimci wani abu da baka dace ka zama mijinta ba ko gobe ne za a daura muku aure da ita tana iya maka tusu.

Akwai wasu maza mayaudara ko makaryata da suke nuna karyar arziki. Sai kuma daga baya budurwa ta gano kamin daurin auren.

Ka jewa mace a mutum. Mace shu’uma ce. Iya gaskiyar ka wajenta iya yadda kake shiga ranta.

  • Mace idan ta hadu da wanda ya fika tana iya sauya shawaran aurenka. Ba ana nufin ya fika kudi ko matsayi ba.

Mata nason kulawa. Da zaran mace ta fahimci wanda ta hadu dashi ya fika kulawa da sakin fuska da iya soyayya da wayewa da bata ‘yanci, yanzu nan zata iya sauya ra’ayinta game da Kai akan auren da kuka yi alkawari.

  • ‘Yan uwa da abokan mace sunada tasiri akanta wajen cusa mata ra’ayi. Idan akayi dacen wacce kake son ka aura tana suraron shawara daga yan uwanta ko abokanta suna iya sauya mata tunani game da kai musamman idan akayi rashin dace taku bazai zo daya ba.

Kada kayi tunanin zasu zo mata da Kalmar ta rabu da kaine kawai ba tare da kawo mata misalan da zasu gamsar da ita ba.

Kamar yadda kake so wacce zaka aura ta samu kyankyawan fahimta da yan uwanka da abokan ka, kaima yanada kyau ka samu hakan da nata idan ba haka ba suna iya sauya mata ra’ayi a kanka.

Da fatan maza masu soyayyar neman aure zasu hankalta. Kamar yadda maza suke sauya ra’ayi akan auren macen da suka mata alkawari, haka suma mata suke.

Leave a Reply

Your email address will not be published.

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

Back to top button