Shugaban Ƙasa Buhari Ya Rusa Hukumar Horar Da Jagoranci Ta Kasa

Daga: Abbas Yakubu Yaura

Shugaban kasa, Mohammadu Buhari ya rusa hukumar gudanarwar cibiyar horar da ‘yan kasa da jagoranci.

A cikin wata sanarwa daya fitar ranar Juma’a, babban sakatare dindindin na ofishin kula da ayyuka Nnamdi Mbaeri, a madadin sakataren gwamnatin tarayya, Boss Mustapha, ya umurci shugaban cibiyar daya mika al’amuran dake bukatar kulawar hukumar ga Ministan Matasa da Ci gaban Wasanni.

Ya kuma ce duk kwamitoci, tare da kwamitocin fasaha da sauran sassan da aka kafa, rusawar ta shafa.

Bayanin ya kasance mai taken, ‘Rushe Hukumar Gudanarwar Jama’a da Cibiyar Horar da Shugabanci’.

An ce, “Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya amince da rusa hukumar gudanarwar cibiyar horar da ‘yan kasa da jagoranci a cikin gaggawa wajen aiwatar da ikon shugaban kasa a karkashin sashe na 5 na kundin tsarin mulkin tarayyar Najeriya na 1999 (kamar yadda aka yi wa gyara) da sashe 4 na Dokar Cibiyar Horar da Jama’a da Jagoranci.

Ganin haka, an umurci Shugaban Cibiyar daya mika al’amuran dake bukatar kulawar Hukumar ga Ministan Matasa da Cigaban Wasanni har zuwa lokacin da za a sake kafa sabuwar hukumar.

“Saboda haka, dukkanin kwamitoci,tare da kwamitocin fasaha da sauran sassan da aka kafa su ma abin ya shafa.”

Leave a Reply

Your email address will not be published.

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

Back to top button