Najeriya za ta dakatar da jiragen ƙasashen da suka hana ‘yan ƙasar shiga ƙasashensu

Daga ranar Talata, 14 ga watan Disamba gwamnatin Najeriya za ta dakatar da jirage daga ƙasashen Birtaniya da Kanada da Saudiyya da Argentina sauka a ƙasar a matsayin ramuwar gayya.

Ministan Sufurin Jiragen Sama Hadi Sirika ne ya sanar da matakin ranar Lahadi a Jihar Legas, yana mai cewa an ɗauke shi ne da zimmar ramuwar gayya kan hana matafiya daga Najeriya shiga ƙasashen saboda nau’in korona na Omicron, kamar yadda kamfanin labarai na NAN ya ruwaito.

Ministan ya ƙara da cewa gwamnati za ta saka Birtaniya da Kanada da Saudiyya da Argentina cikin jerin ƙasashen da za ta haramta wa shiga ƙasar saboda annobar ta korona da kuma yaɗuwar Omicron.

“Kamar yadda suka yi mana, idan har ba za su ƙyale mutanenmu su shiga ƙasashensu ba, to su wa jiragensu za su ɗauka idan suka shigo ƙasarmu?,” in ji shi.

“Mun gama tattaunawa cewa ba za mu yarda ba kuma mun ba da shawara a saka Birtaniya da Saudiyya da Kanada da Argentina cikin jerin dakatattu.”

Leave a Reply

Your email address will not be published.

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

Back to top button