Buhari yana kiran duk malamai domin aje ayi masa nasiha a fa’da masa kuskurensa duk Lokaci – Cewar Sheikh Kabiru gombe

Shugaban Kasa Muhammad Buhari ya yi kira ga dukkan Malamai da suje su yi masa nasiha sannan kuma su sanar da shi kuskuren sa, a dukkan lokacin da bukatar hakan ta taso.

A cikin wani faifai bidiyo da yake yawo a kafafan sada zumunta an ga Shahararran Malamin addinin Sheikh Haruna Kabiru Gombe yana yana fadin damar da shugaba Muhammad Buhari ya bawa Malami.

Domin suna zuwa har cikin fadar sa domin suna yi masa wa’azi tare da yi masa nasiha akan abin da ba dai-dai ba ne domin ya gyara.

Sheikh Kabiru Haruna Gombe ya kara da cewa duk wani lokaci shugaba Bubari yana basu dama domin suje har cikin Fadar sa, domin a sanar da shi a ina kuskuren sa yake.

Malamin ya kara da cewa: Haramun ne shugaba ya bada damar ayi masa nasiha sannan a nuna masa kura kuran sa, amma azo ana zagin da bisa kan manbari.

Ga dai Cikakken bidiyon asha Kallo lafiya.

Leave a Reply

Your email address will not be published.

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

Back to top button