Shugaban Kasa Ya Ce Ya Damu Da Kisan Gillar Da Aka Yiwa Matafiya A Sokoto

Daga: Fahad Kabir Maitata

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya bayyana bakin cikinsa kan kisan gillar da aka yi wa wasu matafiya da ba su ji ba ba su gani ba a jihar Sokoto da ke yankin Arewa maso yammaci kasar.

Cikin wata sanarwar da fadar shugaban ta fitar a ranar Laraba ta ce, shugaban ya ce: “Na damu matuka da yadda waɗannan ƴan kasa da ba su ji ba su gani ba suka gamu da ajalinsu a kan hanyarsu ta neman halal.”

Akalla mutum 21 ƴan bindiga suka ƙona a wata motar fasinja lokacin da suka yi musu kwanton-bauna a ranar Talata.

Sai dai wasu ‘yan uwan fasinjojin sun ce mutanen da ‘yan bindigar suka kona sun kai mutum 42.

Rahotannin sun ce fasinjojin sun fito ne daga karamar hukumar Sabon Birni da ke jihar domin yin ƙaura zuwa wasu yankunan Najeriya, saboda ta’azzarar hare-haren ‘yan bindiga a inda suke.

Buhari ya jajantawa iyalan waɗanda aka kashe tare da alƙalin cewa “jami’an tsaro za su ci gaba da koƙari na kawo ƙarshen waɗannan miyagun mutane”

Ya ce wannan mummunan al’amari da gwamnatinsa ke fuskanta na buƙatar goyon bayan dukkanin ƴan Najeriya.


Follow Hausadrop On Facebook

Leave a Reply

Your email address will not be published.

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

Back to top button