Buhari ya ce za a yi bincike da tabbatar da adalci kan daliban da aka kashe a Legas

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya tabbatar wa ƴan kasar cewa za a yi cikakken bincike kan mutuwar wani ɗalibi da kuma tabbatar da gaskiya da adalci.

Sylvester Oromoni mai shekaru 12 da haihuwa, ana zargin ya mutu ne bayan azabtar da shi a dakin kwanan ɗaliban Kwalejin Dowen da ke Legas a watan da ya gabata, wanda ya yi sanadin ajalisan.

Buhari ya yi Allah wadai da al’amarin, a wata sanarwar da fadarsa ta fitar a ranar Alhamis, tare da alƙawalin cewa zai kasance sanadin kawo ƙarshen matsalar kungiyar asiri da kuma cin zarafin ɗalibai a makarantu.

Shugaban ya kai ziyara Legas a ranar Alhamis babban birnin kasuwanci na Najeriya domin ƙaddamar da wasu ayyuka, ciki har da ƙaddamar da wani littafi wanda Chief Bisi Akande ya rubuta.

Iyayen yaron sun zargi wasu manyan ɗalibai na kwalejin da cin zarafin ɗansu saboda ya ƙi shiga ƙungiyar asiri.

Al’amarin ya sa an rufe makarantar, kuma shugabannin makarantar waɗanda da farko suka ce yaron ya samu rauni ne wurin ƙwallon ƙafa, a watar sanarwa da suka fitar daga baya sun ce sun fara bincike kwana guda bayan kiran da iyayen suka yi kuma ya mutu a ranar.

An shirya gudanar da wani tattaki a ranar Juma’a na nuna fushi kan al’amarin.

Leave a Reply

Your email address will not be published.

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

Back to top button