‘Zan Daina Neman Aikin Gwamnati Idan Na Samu N5m’

Wani tsohon dalibin Jami’ar Maiduguri (UNIMAID) ya ce zai daina neman aikin gwamnati matukar ya samu  kyautar Naira miliyan biyar.

Tsohon dalibin, mai suna Galadima M. Kauji wanda ake wa lakabi da Musaddiq, ya bayyana cewa Naira miliyan biyar ta ishe shi ya kafa kasuwancin da ba sai ya nemi aikin gwamnati ba a rayuwarsa.

Matashin ya kara da cewa, idan har aka ba shi Naira miliyan biyar, daga baya aka gan shi yana neman aikin gwamnati, to a kona takardun shaidar kammala karatunsa.

Ya bayyana haka ne a Facebook, lokacin da yake tsokaci a kan wata tambayar da Aminiya ta yi a shafinta game da abin mutum zai yi idan ya samu Naira miliyan biyar.

Galadima ya ce, “Kasuwa zan fara da ita, shike nan na daina neman aikin gwamnati ke nan, wanda yake daidai da jiran gawon shanu.”

Leave a Reply

Your email address will not be published.

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

Back to top button