Tsohon Shugaban Shi’a da ya bukaci a yi gyara a cikin Al-Qur’ani yayi ridda ya koma addinin Hindu

Tsohon shugaban UP Shia Waqf, Waseem Rizvi, wanda ya bukaci a yi gyara a cikin Al-Qur’ani Mai Girma, yayi ridda ya koma addinin Hindu.

Related Articles

Tsohon shugaban kungiyar dake Uttar Pradesh, yace ya yi Sallama da addinin Musulunci ne a ranar Litinin inda ya tsunduma cikin addinin Hindu.

Rizvi ya koma addinin Hindu da taimakon Swami Yati Narsinghanand, shugaban wajen bauta na Dasna Devi dake Ghaziabad, Uttar Pradesh. Narsinghanand ya bayyana cewa Rizvi zai canja sunansa zuwa Jitendra Narayan Singh Tyagi, bayan fitar sa daga Musuluncin.

A wata hira da yayi da gidan talabijin na Today TV, Rizvi ya ce an cire shi ne daga addinin Musulunci, kuma aka sanya kudi akan duk wanda ya kashe shi, inda aka dinga rubanya kudin a kowacce ranar Juma’a. Sai dai a cewar shi, daga wannan lokaci zai rungumi Sanatan Dharma.

Sai dai kuma, shugaban addinin Hindu na kasar India, Swami Chakrapani Maharaj ya kara tsohon Malamin addinin Musuluncin, inda ya ce shawarar da Wazeem Rizvi ya yanke ta karbar addinin Hindu, kowa da kowa na maraba da shi a cikin addinin.

Ya kara da cewa Waseem Rizvi ya riga ya zama daya daga cikin ‘yan addinin Hindu, saboda haka babu wani da ya isa ya fito ya yi wata Fatwa akan shi. Bama wannan ba, ya kuma bukaci gwamnati da ta tabbatar da tsaro akan shi, domin kare lafiyar shi.

An fara yiwa Waseem Rizvi barazanar kisa ne tun lokacin da ya bukaci kotun koli ta kasar da ta bada damar cire wasu Ayoyi daga cikin Al-Qur’ani Mai Girma, inda a cewar shi Ayoyin suna koyar da tashin hankali. Sai dai kuma yayi rashin sa’a domin kuwa kotun kolin tayi fatali da wannan bukata ta shi.

Ban da wannan ma, Rizvi ya jawo kace-nace matuka a shekarun baya, bayan ya buga wani littafi da a cikin shi ya ci zarafin Manzon Allah (SAW).

Jim kadan bayan wannan kace-nace, da kuma barazanar da aka dinga yi masa kan abubuwan da yayi, Rizvi ya dauki kan shi a wani bidiyo, inda ya bayyana cewa idan ya mutu baya so a binne shi, maimakon haka yana so a kone gawar shi, kamar yadda addinin Hindu ya koyar. Haka kuma ya bayyana cewa yana so a mika gawar shi ga abokanan shi ‘yan addinin Hindu.

Leave a Reply

Your email address will not be published.

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

Back to top button