Gwamnatin Tarayya Ta Shirya Cefanar Da Magudanan Ruwa 12 Na Kasar

Daga: Nura Ahmad Hassan

Gwamnatin tarayya ta ce ta shirya sayar da magudanan ruwa guda 12 na kasar nan domin ba su damar gudanar da aikinsu yadda ya kamata.

Daraktan ayyuka da dubawa a ma’aikatar albarkatun ruwa ta tarayya Mista John Ochigbo ne ya bayyana hakan a wani taron manema labarai ranar Laraba a Benin.

Ya yi wannan jawabi ne a taron manema labarai a matsayin wani bangare na ayyuka a taron ruwa na kasa karo na 10 da ke cigaba da gudana inda ya wakilci minista, Mista Suleiman Adamu.

Ochigbo ya ce sayar da magudanan zai ba su damar samun karin kudaden shiga ga gwamnati.

Ya ba da tabbacin cewa manyan ababen more rayuwa da ake da su a Basins za su ba da tabbacin dawowa kan saka hannun jari.

Ya ce gwamnatin tarayya ta amince da sayar da rafukan ne domin tabbatar da cewa sun samu cigaba mai dorewa da gudanar da ababen more rayuwa.

“rafun suna da manya-manyan ababen more rayuwa kamar tsarin samar da ruwan sha, madatsun ruwa da na ban ruwa da ke bukatar kudade masu kyau don samun damar cigaba da gudanar da ayyukansu da kuma samar da riba ga ‘yan Najeriya.

JaridaralkIblah ta rawaito yana cewa “Muna gayyatar kamfanoni masu zaman kansu don gane da wannan damar da aka bayar,” “in ji shi.


Follow Hausadrop On Facebook

Leave a Reply

Your email address will not be published.

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

Back to top button