Innalillahi: Garin rage mata hanya, an sace yarinya mai shekaru 5 a jihar Kano

Jihar Kano – An sace wata yarinya ‘yar shekara biyar mai suna Hanifa Abubakar a unguwar Kawaji da ke Kano a ranar Asabar.

Related Articles

Masu garkuwa da mutane ne suka yi awon gaba da ita ne a cikin a babur din dai-daita sahu yayin da suka yaudare ta da sunan rage hanya

Daily Nigerian ta tattaro cewa lamarin ya faru ne da karfe 5 na yamma lokacin da yarinyar da sauran yaran unguwar suke dawowa daga makarantar islamiyya.

Kawunta, Suraj Zubair ya ce:

Kawunta, Suraj Zubai ya ce:Kawunta, Suraj Zubai ya ce:

“Nisan dake tsakanin gidansu zuwa makarantar Islamiyyae bai da yawa. Don haka yara sukan yi tattaki zuwa makaranta da kansu.

“A cewar wasu yaran da lamarin ya faru a gaban idanunsu, masu garkuwa da mutanen sun zo ne a cikin a dai-daita sahu suka ce za su kai su gidansu. Bayan saukarsu ne suka ce Hanifa ta sake shiga domin sake dana ta, daga nan suka tsere da ita.

“Ina so in yi amfani da wannan kafar domin yin kira ga wadanda suke da wani bayani game da inda Hanifa take da su tuntubi ofishin ‘yan sanda mafi kusa ko su kira wannan lambar: 08032668195.”

Unguwar Kawaji a karamar hukumar Nassarawa na daya daga cikin unguwannin da ake fama da matsalar satar yara a Kano.

A cikin unguwar a baya, an yi garkuwa da Yusuf Nasiru dan shekara 9 a ranar 28 ga watan Disamba, 2020 bayan ya dawo daga makarantar Islamiyya da rana.

Idan za a iya tunawa, a watan Oktoban 2019, rundunar ‘yan sandan jihar Kano ta kama wasu gungun masu garkuwa da mutane shida bisa zarginsu da yin garkuwa da yara, da sayar da su da kuma tursasa musu karbar addinin kirista a garin Onitsha na jihar Anambra.

Biyo bayan yawaitar sace yaran Kano da aka yi a shekarun baya tare da kubutar da wasu daga cikinsu a Kudancin kasar nan, Gwamna Abdullahi Ganduje ya kafa wani kwamitin bincike.

Manufar kwamitin shi ne ya binciki yadda ake tauye hakkin yaran da aka ceto tare da bankado duk irin wadannan lamura daga shekarar 2010 zuwa yau a jihar.


Follow Hausadrop On Facebook

Leave a Reply

Your email address will not be published.

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

Back to top button