Yadda Rayuwar Rahama Haruna Takasance Acikin Bokiti Har Allah Ya Karɓi Rayuwarta

Rahma Haruna ‘yar Jihar Kano Najeriya ce
yar shekara 19 da labarin ta ya shahara
tunda wani hoto da mai daukar hoto Sani Maikatanga ya dauki hotunanta.

An haifi Rahma Haruna wani lokaci tsakanin1996 zuwa 1997, A Birnin Kano Najeriya, tana da shekara shida Rahama kafafuwanta da hannayenta suka daina girma, ta kamu da Wata cuta da ba a san irinta ba, wanda yasa tanakasa, ba ta iya yin ayyukan yau da kullun kamar tafiya, rarrafe ko ma sarrafa yawancin kayayyaki.

Sai dai ta ci gaba da zama a cikin bokitin roba, jim kadan bayan hoton ya fara yaduwa, wani da ba a bayyana sunansa ba ya bata kyautar keken guragu don saukaka jigilar ta.

lyayen Rahama sun tabbatar da cewa sun kashe kusan naira miliyan 1 wajen nema mata lafiya amma abin yaci tura.

Rahama ta rasu ne a ranar 25 ga Disamba, 2016 tana da shekaru 19 a Kano, Najeriya, taa rasu ta bar iyayenta da ‘yan uwanta Daga B. Salia Sicey.

Toh Allah Ya Jikanta Ya Gafarta Mata Idan Tamu Tazo Allah Yasa Mu Cika Da imani, Zamu So Mu Karbi Ra’ayoyinku A Sashenmu Na Tsokaci Akan Wannan Baiwar Allah, Sannan Kada Ku Manta Ku Danna Alamar Kararrawa Domin Samun Sababbin Shirye-shiryenmu Akoda Yaushe Mungode.


Follow Hausadrop On Facebook

Leave a Reply

Your email address will not be published.

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

Back to top button