Muddin Farashin Mai Yakai 340 Sena Dena Cin Abinci Cewar Wani Matashi A Kano

Wani matashi yayi barazanar shiga yajin aikin cin abinci na din din din, muddin aka kara kudin man fetir daga 163 zuwa 340.

Matashin dai dan asalin jihar Kano dake Arewa maso yamma a Nigeria yayi wannan barazanar ne jin kadan bayan samun tabbacin karin kudin man a sabuwar shekarar da za’a shiga nan da makonni 4.

A watan daya gabatane dai Gwamnatin taraiya ta bada sanarwar cewa akwai yiyuwa tai karin farashin man wanda zuwa 340 duk lita sabanin 163 da ake siyarwa.

Sedai al’umma da dama wannan sanarwar batai musu dadi ba musamman masu karamin karfi inda suke kallon abun akansu zai kare, kamar yadda wani dattijo ya baiyanawa wakilin sarewa hausa cewa “koba komai babu wata hanya akasarnan da tallafin Gwamnati ke zuwa ma talaka kai tsaye illa ta tallafin man fetir din, kuma idan aka cire tallafin to talakawa ire irena zamu gala baita kwarai” acewar sa.

Wannan dai shine karo na uku da Gwamnatin Muhammadu Buhari zatayi karin kudin man fetir din tun bayan darewar sa kan karagar shugabancin kasar a shekarar2015.

Inda ya samu ana saida litar man fetir akan 85, sai dai ansamu kare karen kudin ne bisa faduwa da tattalin arzikin kasar ya ringayi akai akai.


Follow Hausadrop On Facebook

Leave a Reply

Your email address will not be published.

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

Back to top button