Buhari Ya Tafi Dubai Tare Da Rakiyar Ministoci 10

Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya kama hanyar zuwa birnin Dubai na Hadaddiyar Daular Larabawa domin halartar taron bajelolin kasuwanci

Kakakin Shugaban, Femi Adesina ne ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa ranar Laraba.

Ya ce Buhari zai samu rakiyar Ministocin Harkokin Waje da Kasuwanci da Masana’antu da ta Kudi, Kasafi da Tsare-tsare da na Tsaro da na Sufurin Jiragen Sama da kuma na Noma da Raya Karkara.

Sauran sun hada da Ministan Lafiya da na Sadarwa da Tama da Karafa da Minista a Ma’aikatar Kasuwanci da mai ba Shugaban Kasa shawara kan harkokin tsaro da Shugaban Hukumar Leken Asiri ta Kasa (NIA) da kuma Shugabar Hukumar Kula da ’Yan Najeriya mazauna ketare.

Adesina ya ce taron, wanda aka yi wa lakabi da EXPO 2021, zai ba Najeriya damar bin sahun kasashe kimanin 190 wajen kawo ci gaba da kuma walwala ga kowa.

Ya kuma ce taron zai bayar da dama ga wakilan Najeriya su nuna wa sauran kasashen damar da kasar ke da ita wajen zuba jari.

Kakakin Shugaban ya kuma ce Buhari zai tattauna da masu sha’awar zuba jari da kuma Sarkin Abu Dhabi, Sheikh Mohamed bin Zayed Al Nahyan, da kuma Mataimakin Shugaban Hadaddiyar Daular Larabawa, Sheikh Mohammed bin Rashid Al Maktoum.

Leave a Reply

Your email address will not be published.

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

Back to top button