An Sami Raguwar Masu Ɗauke Da Cuta Mai Karya Garkuwar Jiki HIV A Kano

Daga: Nura Ahmad Hassan

Gwamnatin jihar Kano ta ce a kokarin da gwamnatin ke hadin gwiwa da kungiyoyin da ma ‘yan jarida zuwa yanzu an sami cigaba kwarai da gaske akan yaduwar cuta mai karya garkuwar ta kamjamau wato HIV, domin alkaluma sun nuna.

Kwamishinan lafiya na jihar Kano Dr. Aminu Ibrahim Tsanyawa ya bayyana haka a ganawarsa da manema labarai yau kan ranar masu fama da larurar annobar cuta mai karya garkuwar jiki HIV, ya ce “Alkaluma sun nuna cewa an sami raguwar masu dauke da wannan cuta ta HIV daga kaso 2.5 zuwa kaso 0.5 wanda wannan ba karamin cigaba ba ne aka samu kan yanda ake yaki da wannan annoba ta HIV a fadin wannan jiha.

Kwamishinan ya ce “mutane sama da dubu 35 suna shan magani a fadin jihar Kano a cibiyoyin da aka ware don karbar magunguna kyauta, gwamnatin jihar Kano ta ciri tuta kan yadda tayi tsare-tsare domin yaki da wannan cutar baki da a fadin jihar, ta samar da cibiyoyi 600 domin a dakile yaduwar wannan cuta daga uwa zuwa Danta, wanda wannan zai rage yaduwar wannan cuta.

Ya ce a cigaba da tsare-tsare akan makon yaki da wannan cuta Maidakin gwamna Farfesa Hafsat Ganduje zata Kaddamar da abubuwa daban-daban don kula da masu fama da wannan cuta ta HIV a jihar, daya daga ciki akwai fadakarwa da lakcoci da tsare-tsaren tallafawa masu wannan cuta don su kula da kansu da kula da Iyalansu.

Tsayawa ya kuma ce ana cigaba da gyara manyan asibitin jihar don inganta kula da lafiya, a don haka ne gwamnatin ta samar da hukuma guda don inganta kula da lafiya a fadin jihar Kano, da cigaba da horar da ma’aikatan lafiya.


Follow Hausadrop On Facebook

Leave a Reply

Your email address will not be published.

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

Back to top button