EFCC Ta Kama Yan Yahoo 60 Yayin Taron Karrama Gwanayen Cikinsu

Jami’an hukumar yaki da masu yiwa tattalin arzikin kasa ta’’annati wato EFCC reshen Jihar Legas sun kama wasu mutane sittin {60} da take zargi da Zamba ta intanet a wani taro Karramawa da suka shirya a dakin taro na wani otel dake garin Abeokuta a Jihar Ogun.

Binciken hukumar EFCC ya gano cewa an shirya taron ne don karrama wasu shahararrun matasan da suka yi fice a harkar zamba ta intanet da aka fi sani da ‘yahoo boys.’ Wanda kuma anan ne jamián hukumar sukaa yi nasarar cika hannun su da matasan.

Wata sanarwa da hukumar ta wallafa a shafinta na Internet ta bayyana cewa jamián ta sun kuma gano wasuu abubuwa na musamman tare da su, wadanda suka hadar da motoci masu tsada, wayoyi masu tsada da kwamfiyutoci. Kuma sanarwar ta bayyana cewa Za’a gurfanar da su a gaban kotu da zarar hukumar ta kammala bincike a kan su.


Follow Hausadrop On Facebook

Leave a Reply

Your email address will not be published.

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

Back to top button