85 Cikin 100 Na ’Yan Najeriya Ba Su Da Gaskiya – Sheikh Giro Argungu

Fitaccen malamin Musulunci, Sheikh Abubakar Giro Argungu, ya ce kashi 85 cikin 100 na ’yan Najeriya ba su da rikon amana.

Sheikh Giro ya bayyana haka ne a wurin wani taron wa’azi, inda ya bukaci ’yan Najeriya da su nesanci cin hanci sannan su rungumi adalci da tsare gaskiya.

Malamin ya kuma roki ’yan kasar da su dage da rokon neman Allah Ya kawo karshe matsalar tsaro da ta addabi kasar.

Ya bayyana cewa yin hakan shi ne mafitar da za ta kawo aminci da hadin kan kasa da ake bukata domin ci gaban Najeriya.

Shehin malamin ya ce, idan ’yan Najeriya suka dage da rokon Allah, to Allah zai kawo karshen ayyukan ’yan bindiga, Ya kuma kawo aminci da ci gaba mai dorewa a kasar.

Ya yi kiran ne a wanin taron wa’azi da aka gudanar a garin Umaisha da ke Karamar Hukuma Toto ta Jihar Nasarawa.

An shirya taron wa’azin ne domin murnar daurin auren Shugaban Majalisar Dokokin Jihar Nasarawa, Ibrahim Balarabe Abdullahi da matarsa ta uku, Rukaiyat Mohammed.

Leave a Reply

Your email address will not be published.

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

Back to top button