Banga Wanda Yakai Shugaban Kasa Muhammadu Buhari Gaskiya A Nigeria Ba – Rarara

Daga: Fahad Kabir Mai Tata

Fitaccen mawakin siyasa a Nigeria daga masana’antar fina finan Hausa ta Kannywood dan asalin jihar Katsina, Dauda Adamu Kahutu Rarara ya ce baiga wani wanda ya kai shugaban Nigeria Muhammad Buhari Gaskiya ba a kasar.

Dauda wanda yayi wannan jawabi da yammacin ranar Asabar yayin da yake zantawa da manema labarai a jihar Kano, ya kara da cewa a fanin baba Buhari ko gwamnan jiharsa ta Katsina Masari baya fadar wani abu na son rai, tsantsar gaskiya yake fada akansu.

“Sau dayawa ina duba wanda suke sauraran wakata ne idan zan rubuta bawai na kalli su da zan yiwa ba”

“Kuma dalilin da yasa nafi yiwa Masari da Buhari wake shine, banga wanda ya kai Muhammadu Buhari Gaskiya ba a Nigeria kuma banga wanda ya kai Masari iya siyasa ba a jihar Katsina” acewar Dauda.

Daka karshe ya ce, maganar tsi-tsi da mutane suke tayi dama ai bazaka iya hana jariri kukaba indai bazaka bashi abinci ba, domin an kwashe shekara 16 ana barna a Nigeria, ga rashin kudin shiga, ga Korana duk idan aka kalla sun taimaka wajan tsintar kai a halin da ake ciki yanzu ba wai shugaban kasa bane.

Leave a Reply

Your email address will not be published.

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

Back to top button