Da Dumi-Dumi: Dalibar Jami’ar BUK ta mutu tana tsaka da Sallah a dakin kwanan dalibai

Kano – Wata daliba dake ajin ƙarshe a tsangayar Ilimi ta jami’ar Bayero dake Kano (BUK), Binta Isa, ta rasu a ɗakin kwanan dalibai ranar Jumu’a 26 ga watan Nuwamba, 2021.

Ɗalibar wacce ta fito daga jihar Kogi, ta rasa rayuwarta ne da misalin ƙarfe 7:00 na dare bayan fama da gajeruwar rashin lafiya da ta danganci ciwan ƙirji.

A cewar daraktan lafiya na jami’ar, wanda ya tabbatar da aukuwar lamarin, Binta ta je Asibitin jami’a na New Campus a ranar 24 ga watan Nuwamba, inda ta yi korafin tana fama da ciwan ƙirji.

Ya ƙara da cewa jami’an da suka duba mamaciyar a lokacin, sun bata magani tare da zayyana mata yadda zata yi amfani da su.

Daraktan ya bayyana cewa daga nan Binta ta samu sauki, domin ta cigaba da halartan Lakca ranar Alhamis da Jumu’a, kuma ta cigaba da ayyukan karatunta.

Yace:

“A ranar Jumu’a 26 ga watan Nuwamba, 2021 da yamma, lokacin sallar Magriba, ta shaida wa abokiyar zaman ɗakinta cewa tana jin ciwan ƙirji, amma a haka ta kokarta ta yi Alwala domin ta yi sallar Magrib a ɗakin.”

“Abokan zamanta a ɗakin sun kaɗu kuma sun tsorata da suka dawo suka tarad da ita ta yi warwas a ƙasa.”

“Nan take suka sanar da mutane, akai gaggawar kaita asibitin koyarwa na Aminu Kano, inda likita ya tabbatar da cewa ta rasu.”

Wannan na kunshe ne a wata sanarwa da jami’ar ta fitar, ɗauke da sa hannun mataimakin rijistara, Lamara Garba, kuma Legit.ng Hausa ta samu kwafin takaradan.

Jami’a ta sanar da iyalan dalibar

Mataimakin shugaban BUK, Farfesa Sagir Adamu Abbas, tare da rijistara, Jamil Ahmad Salim, daraktan lafiya da darakan tsaro, Abdulyakin Ibrahim duk sun halarci wurin da lamarin ya faru.

A halin yanzun jami’a ta sanar da ɗan uwan ɗalibar, wanda yake zaune a cikin garin Kano, game da lamarin da ya faru

BUK ta yi jimamin wannan rashi

VC Farfesa Adamu, a madadin jagororin BUK, malamai da ɗalibai, ya bayyana damuwarsa da rasuwar matashiya Binta Isa, wacce ta mutu ta na gab da kammala karatunta.

Ya kuma mika ta’aziyya ga iyayenta, yan uwa da abokan karatu, kuma ya yi addu’a Allah ya yafe mata kura-kuranta, ya sa tana daga cikin yan Aljanna. A wani labarin kuma.

Source: Legit Hausa

Leave a Reply

Your email address will not be published.

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

Back to top button