Gidan Jaridar Aminiya Zata Dauki Ma’aikata
Shahararren gidan jaridar nan mai suna AMINIYA (Daily Trust) ya sanya cewar zata dauki ma’aikata a bangaren aikin jarida na zamani wato Digital Journalism domin kara bunkasa aikinta na jarida.
Kamfanin zai dauki ma’aikatan dake da kwarewa a bangaren dasuka shafi wadannan abubuwa kamar haka:
- Aikin jarida da amfani da kafafen yada zumunta
- Zakulo labarai da tantance su gami da bibiyar al’amura da fahimtar harkar yada labarai ta hanyar kafofin zamani
- Iya karanta da rubuta Hausa da Turancin ingilishi
- Sanin abin da masu karatun labaran Hausa suke so
- Amfani da manhajar gyara gyara hoto, bidiyo ko sauti
- Ana bukatar akalla shaidar karatu ta HND ko degree na farko
- Aikin kwantarage ne a Abuja ko Kano
Idan kuna ganin kun cancanta, ku aiko da takardunku ta: aminiyasicial@dailytrust.com
Allah ya bada sa’a