Da ana sayen rai da kudi, da mun ceto Sani Dangote – Tinubu

Jagoran Jam’iyyar APC a Najeriya Bola Ahmed Tinubu yace da ana sayen rai da kudi, da sun ceto ran kanin Aliko Dangote, wato Sani Dangote da ya rasu a wannan mako.

Hausa Drop ta rawaito Tinubu ya bayyana haka ne yayin da yake jawabi lokacin da ya kai ziyarar ta’aziya gidan Alhaji Alhassan Dantata dake birnin Kano da kuma iyalan Dangote.

Tinubu yace da ana biyan kudi dan ceto rai, da zasu kaddamar da gidauniyar ceto ran Alhaji Sani Dangote saboda kyawawan halayen sa.

Tsohon gwamnan Lagos ya bayyana mutuwa a matsayin wani ikon Allah, wadda babu yadda za’ayi a musanya ta da kudi kuma babu yadda ‘dan adam zai yi idan lokacin sa yayi kamar yadda Ubangiji ya tanada.

Tinubu ya bayyana Sani Dangote a matsayin mutumin Lagos wanda ya bada gagarumar gudumawa wajen ci gaban birnin wanda suke alfahari da shi, yayin da ya roki Allah Ya gafarta masa.

Rasuwar Sani Dangote ta girgiza wan sa Aliko Dangote, attajirin da yafi kowa dukiya a Afirka, wanda yace a idan su ‘dan uwan na sa ya rasu bayan yayi fama da doguwar rashin lafiya.

Aliko yace likitoci sun shaida musu cewar a cikin sa’a guda Sani zai rasu, kuma mahaifiyar su da ‘yayan marigayin na kallon yadda ran sa ya fita daga jikin sa.

Attajirin yace ziyarar da mutane keyi Kano suna mika sakon ta’aziyar su na taimakawa wajen rage musu radadin mutuwar da suke ji.

Cikin wadanda suka ziyarci Kano domin gabatar da ta’aziyar su ga Aliko Dangote sun hada da Mataimakin shugaban kasa Yemi Osinbajo da shugaban majalisar dattawa Ahmed Lawal da shugaban majalisar wakilai Femi Gbajabiamila da gwamnonin jihohi da sarakuna da kuma malamai.

Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewar Tinubu ya samu rakiyar Gwamnan Kano Abdullahi Ganduje lokacin ziyarar kamar yadda rif ta wallafa.


Follow Hausadrop On Facebook

Leave a Reply

Your email address will not be published.

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

Back to top button