Wani sabon al’amari ya bulla akan naiman taimakon al’umma ga jinyar jarumin kannywood Sani Garba SK

wasu daga cikin jaruman kannywood sun tai kamaki “Sk” mutane suna ta turo min wannan video na Sani Sk akan mu taimaka masa, to magana ta gaskiya a kwanakin baya ma mun yi posting Sani Sk.

Kuma wasu daga cikin yan fim sun taimaka masa kuma suna kan ci gaba da taimala masa da al’umar gari, sai dai cutar shi mai cin kudi ce wato ciwon sugar da ciwon hanta.

Ga wanda suka ta makar yanzu haka abdulamart_mai_kwashewa, ya Bashi Dubu Dari biyar, ya sa kuma an kai shi asibiti, adizatou, ta bashi Dubu Dari Biyu da Hamsin.

realalinuhu, ya bashi Dubu Dari, da wasu da yawa da suka bayar daga masana’antar Kannywood din, muna adduar Allah ya saka musu da alkairi.

Kamar yadda muke fada ciwon Sani Sk ciwo ne mai cin kudi, Yan fim suna iyakacin kokarinsu, amma kuma al’umma dan’uwanku ne musulmi.

Wanda wannan yan’uwantakar ta fi ta sanaa za ku iya taimakawa ba tare da cin mutunci kowa ba. Allah ya ba shi lafiya.


Follow Hausadrop On Facebook

Leave a Reply

Your email address will not be published.

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

Back to top button