Hisba Ta Kai Sumame A Wajan Taron Zaben Sarauniyar Kyau A Jihar Kano

Daga: Nura Ahmad Hassan

Hukumar Hisbah a jihar Kano, ta baiyana kudirin cigaba da kai sumame a kai a kai dukkan wuraren da a ke zargin samari da “yan mata kan hadu, domin aikata badala.

Babban Dataktan hukumar, Dr. Aliyu Musa Aliyu Kibiya shine, ya furta kudirin a ranar Litinin a shalkwatar hukumar da ke unguwar Sharada a birnin Kano.

Wannan ya biyo bayan wani sumame da dakarun hukumar su ka kai a wurin shakatawa na (NITEL training centre) da ke kan titin Katsina kusa da Hajji camp.

Dr. Aliyu Musa Aliyu Kibiya ya cigaba da cewar, duba da yadda dakarun hukumar ke cigaba da artabu da irin wadan nan samari da yan mata a wurare daban – daban a sassan kwaryar birnin Kano.

Ya kara da cewar, ko da iyaye sun saki yayan su sa – sakai to hukumar ba zata bari ba, kuma za’a cigaba da daukan matakan babu sani – babu sabo.

Kazalika burin hukumar bai wuce dukkan taga al’uma a jihar sun zama na gari ba, masu yin biyayya ga dokokin Allah madaukakin sarki.

A karshe Aliyu ya yi addu’ar Allah ya shiryar da matasan jihar maza da matandomin daga cikin su za’a sami shugabani a nan ga ba.

A lokacin sumamen, hukumar Hisbah sun samin nasarar kamo yan mata 11 da saurayin da ya hada bikin zaben sarauniyar kyau, a filin shakatawa na NITEL training centre, ciki har da kwalaben nau’ikan barasa har guda 324, kimanin katon 40.


Follow Hausadrop On Facebook

Leave a Reply

Your email address will not be published.

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

Back to top button