Yanzu Hadiza Gabon Ta Wallafa Bidiyon Malam Isah Ai Pantami A Shafinta Wanda Ya Birgeta Gaskiya Ta Bayyana

Kamar Yadda Kuka Sani A ‘Yan Kwanakin Nan Ake Ta Yada Labarai Marasa Tushe Game Da Soyayyar Malam Isah Ali Pantami Da Hadiza Gabon, Yadda Har Wasu Suke Cewa Zai Aureta.

Fitacciyar Jarumar Film Din Hausa Ta Kannywood Hadiza Gabon Ta Wallafa Bidiyon Malam Isah Ali Pantami A Shafinta Na Instagram Wanda Ya Birgeta.

Acikin Bidiyon Munga Malamin Yana Wa’azi Akan Rayuwa, Yadda Yake Bayyana Cewa Babu Wanda Ya Isa Ya Kashe mutum Face Da Yardar Allah, Sannan Kuma Kada Komai Ya Tsorataka, Domin Rayuwarka Tana Hannun Allah.

To Sai Dai Wannan Abunda Jarumar Tayi Wasu Daga Cikin Mabiyanta Sunyi Zaton Wani Abu, Duba Da Yadda Ake Ta Cece Kuce Akan Lamarinnasu Na Batun Soyayya Ko Kuma Aure.

Yadda Har Wasu Daga Cikin Mabiyan Jarumar Suke Zaton Cewa, Ko Wannan Jita-jitar Ta Isa Kunnen Hadiza Gabon Har Ta Dauki Bidiyon Malamin Ta Wallafashi A Shafinta Ga Bidiyon Sai Ku Kalla.

Wannan Ya Saka Dayawa Daga Cikin Mabiyan Jarumar Suna Zaton Cewa Kamar Akwai Kamshin Gaskiya Game Da Abunda Ake Zato.

Toh Amma Sai Dai A Wani Bincike Da Mukayi, Mun Gano Cewa Wa’azin Malaminne Ya Birgeta Yadda Yake Bayani Akan Mutuwa Da Kuma Rabo, Domin Kuwa A Yanzu Muna Wani Hali Na Tsoron Mutuwa Duba Da Yadda Sha’anin Kasa Ya Kasance Na Rashin Tsaro.

Hakane Yasaka Mutane Da Dama Suke Tsoron Mutuwa, Yadda Har Wasu Suke Katsewa Hanyoyin Sadarwarsu Saboda Gudun Masu Garkuwa Da Mutane, Wasu Ma Har Wannan Tsoron Yana Taba Hanyar Cin Abinchinsu Wato Kasuwanchi.

Amma Kuci Gaba Da Kasancewa Damu Da Zarar Abu Ya Gama Tafiya Kuma Mun Gama Bincike Akan Al’amarin Zamu Bayyana Muku Gaskiya Game Da Hakan, Hanya Mai Sauki Ce Da Zaku Kasance Damu A Koda Yaushe Ita Ku Danna Alamar Kararrawa Da Take Da Jar Kala A Kasa Domin Da Zarar Mun Saki Sabon Labari Zaku Ganshi Sai Ku Saurara Ko Ku Karanta Mungode.

Sannan Zamu So Ku Ajiye Mana Ra’ayoyinku A Sashenmu Na Tsokaci Akan Wannan Labari.


Follow Hausadrop On Facebook

Leave a Reply

Your email address will not be published.

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

Back to top button