Innalilahi wainna ilaihir raji’un mayaƙan (ISWAP) sun kashe wani birgediya janar na sojojin Nigeria a wani bata kashi da aka fafata a jihar Barno a yau.

Mayakan ISWAP sun harbe wani Birgediya Janar din soji a wani hari na kwanton bauna da suka kai Jihar Borno.

Idan bamu mantaba a ɗazune mukakawomuku rahoton jihar Borno a yanzuma ga saban rahotan da muka samu daga ɗaya daga cikin manema labaranmu na jihar Barno.

Rahotanni sun bayyana cewa an kuma kashe wasu sojoji hudu yayin harin da ya auku a Bulguma wani yanki mai tazarar kilomita kadan da garin Askira na Karamar Hukumar Askira Uba da ke Borno.

Bayanai sun ce mayakan sun yi wata rundunar hadin gwiwa daga garin Chibok kwanton bauna da aka tura dakarunta domin kai dauki yankin da lamarin ya faru.

Wata majiya ta ce sojojin sun furta cewa yau rana ce ta bakin ciki a gare mu da muke nan filin daga domin kuwa mun rasa babban Kwamanda mai mukamin Birgediya Janar.

Birgediya Janar din da sojoji hudu sun rasa rayukansu yayin da suke kai hanyarsu ta kai wa sojoji dauki a garin Askira da mayakan ISWAP suka yi wa dirar mikiya a cewar majiyar.

Cikin wata sanarwa da Mai magana da yawun rundunar sojin kasa na Najeriya Birgediya Janar Onyema Nwachukwu ya fitar a yammacin Asabar ya bayyana lamarin a matsayin abun takaici

Ya ce Babban Hafsan Sojin Kasa na Najeriya Laftanar Janar Faruk Yahaya ya jajanta wa iyalan sojojin da suka riga mu gidan gaskiya a harin.

Muna kira da a turo jiragen yaki su taimaka wa dakarun da ke kasa, maharan sun fi mu yawa motocin yaki biyar kawai gare mu inji Yakubu wanda suka ragemana.

To jama’a zamuso mukarɓi ra ayoyin Ku na sakon ta aziyya ga iyalan Nigeriya janar don jin tabakinku zaku iya biyomu ta sahinmu na tsokaci.

Leave a Reply

Your email address will not be published.

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

Back to top button