Sai bayan Aure na ga ashe nono daya gare ta, iyayen matata sun yaudare ni, wani Ango ya koka

A yau ne muka sami wani faifai bidiyon daga tashar Tsakar gida dake kan manhajar Youtube, inda a cikin bidiyo mukaji wani labari game da wasu ma’aurata inda mutumin yake bayyana rashin jin dadin sa akan auren da yayi.

Mutumin yayi korafi akan cewa iyayan matar da ya aura sun yaudare shi sabida sun boye masa wani al’amari da yake tattare da ‘yar tasu, sai bayan ya aure ta kuma ya gano wani abu wanda bai yi tsammanin ‘yar tasu tana da shi ba.

Tun kafin ayi auren iyayan yarinyar basu sanar da mutumin cewa ‘yar su nono daya gareta ba, inda suka rufe maganar har sai da aka yi wannan aure tukuna gaskiya ta bayyana.

Inda mutumin ya gano matar tasa nono daya gareta wanda tun farkon haduwar su da matar tasa bai bata tunanin haka take ba sai da sukayi aure, amma ya bayyana cewa iyayan matar tasa sune suka yaudare shi basu sanar da shi ba.

Domin kuji cikekken labari akan wannan hatsaniyar dake faruwa, sai ku kalli bidyon dake kasa.


Follow Hausadrop On Facebook

Leave a Reply

Your email address will not be published.

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

Back to top button