Kuskure Ne Mutum Ya Ji Cewa Shi Akan Daidai Yake, Saura Ba A Daidai Suke Ba

Daga: Muhammad Rabi’u Jogana

Jarumi kuma darakta a masana’antar Kannywood Ibrahim Bala ya bayyana yadda mutum yake kasancewa munafiki ta hanyar kafa hujja da Hadisin Huzaida Ibn Yamaan.

Daraktan ya kara da cewa daga cikin Hadisin “Babu wanda yake tsoron lalacewar aikin sa sai mumuni, haka kuma wabu Wanda yake ganin shine mutumin kwarai sai munafiki”

Kazalika, bai halatta ga wani mutum ya gamsu cewa shi na kwarai ne ba, har yazama bashi da aiki sai magana akan laifukan wasu tare da take nasa, to wannan shine ake kira da munafikin, mai imani kuwa shine wanda damuwarsa kansa da kuma abun da yake aikatawa yana jin kamar shi me laifine sai ya kara gyarawa, ba wanda wasu ke aikatawa ba.

Daga karshe Bala yayi addu’ar neman tsari daga bibiyar laifukan mutane, munafinci, hassad, da kuma ganin gyashi kan wata baiwa da Allah ya yiwa wani cikin bayinsa.

Daraktan ya bayyana hakan ne ashafinsa na sada zumunta na (Instagram) a safiyar fanar Litinin din farkon makon da muke ciki.

Leave a Reply

Your email address will not be published.

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

Back to top button