Jami’an Tsaro Da Ɗan Jarida: Zamu Rubutawa Babban Sufeton Ƴan Sandan Nigeria Takarda

Daga: Fahad Kabir Maitata

Idan har babu sa hannun manyan jami’an tsaro a barnar da ake zargin wani Dan sanda mai suna Friday ya ke yi a jihar Kano, to ya zama lallai kwamishina Sama’ila Sha’aibu Dikko na jihar ya samar da kwamitin bincike na gaggawa akan jami’in da ake zargin kamar yanda doka ta tanada.

Fitaccen Dan gwa-gwarmaya kuma lauya mai zaman kansa a Nijeriya Barista Audu Bulama Bukatar shine yayi wannan kira a daran ranar Juma’a tacikin wani faffan bidiyo da suke tattaunawa kaitsaye a manhajar (Zoom) da Dan jaridar Nasir Salis Zango da Barista Abba Hikima Fagge kan abun da doka tace akan lamarin.

Bukarti ya ce hakika akwai kamshin gaskiya akan wannan jami’i kuma “zamu rubuta takardar ga babban sufeto na ‘yan sandan kasar nan, kuma duk irin barazanar da Friday yake yimaka Nasiru cewa kayi labarin karshe to ya yaudari kanshi domin bayanzu aka fara irin wannan labarin na cin zali ba, kuma bazaka daina ba Insha Allahu” a cewa Barista.

Wannan dambarwa dai ta bulo kaine cikin tsakiyar satin da muke shirin bankwana dashi, inda al’ummar wasu kasuwanni a Kano suke kai Korafin cewa Dan sanda Friday yana zuwa haka kawai ya kamasu ba dalili ko hujja kuma sai sunyi belin kansu da kudi masu yawa, anyi ba sau daya ba wasu an dawo musu da kudin su ammafa ba’a daina ba.

Hakan tasa Dan jarida Nasir Zango ya fara fallasa labarin har takai ga Friday yana yimasa barazana.


Follow Hausadrop On Facebook

Leave a Reply

Your email address will not be published.

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

Back to top button