Gwamnatin Tarayya Zata Fara Baiwa Ƴan Nigeria Alawus Ɗin Sufuri

Daga: Nura Ahmad Hassan

Ministar kudi Kasafi da tsare tsaren kasa Hajiya Zainab Shamsuna Ahmed ta ce gwamnatin tarayya za ta fara biyan ‘yan Najeriya kudaden alawus na sufuri bayan cire tallafin man fetur.

Da take magana a wata hira da aka yi da ita a gidan Talabijin na Channels a ranar Alhamis, Zainab Ahmed ya ce tallafin mai na janyo zirarewar albarkatun kasa da ya kamata a yi amfani da su wajen bunkasa harkar ilimi da lafiya.

Ta bayyana tallafin man fetur a matsayin “babban magudanar ruwa da sharar gida” ga tattalin arzikin kasar, inda ta kara da cewa yana da matukar muhimmanci kasar ta fice daga tsarin bayar da tallafin man fetur.


Follow Hausadrop On Facebook

Leave a Reply

Your email address will not be published.

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

Back to top button