Gaskiya Ta Bayyana Akan Daukan Hoton Da Hadiza Gabon Tayi Da Malam Isah Ali Pantami

Kamar Yadda Kuka Sani A Kwanakin Baya Labarai Sunyi Ta Yawo A Kafafen Sada Zumuntar Zamani Na Maganar Auren Hadiza Gabon Da Malam Isah Ali Pantami, Wasu Kuma Suce Akwai Soyayya A Tsakaninsu.

Sai Dai Bayan Ƙura Ta Lafa Sai Kuma Muka Samu Wasu Hotunan Karya Da Ake Yadawa A Kafafen Sada Zumuntar Zamani, Musamman A Shafin Facebook Da Instagram Ga Yadda Hotunan Suke.

Wannan Hoton Da Kuke Gani Na Malam Isah Ali Pantami Da Hadiza Gabon Ba Gaskiya Bane, Domin Munyi Dogon Bincike Akan Lamarin Sannan Kuma Mun Gano Gaskiyar Al’amari, Ga Yadda Hoton Yake.

Wannan Shine Asalin Hoton Malam Isah Ali Pantami Da Wani Mutumi, Sai Akayi Amfani Da Hoton Hadiza Gabon Dake Kasa Kamar Haka Aka Cire Wannan Mutumin Na Kusa Da Malam Isah Ali Pantami Aka Saka Hoton Hadiza Gabon Ga Hoton Da Akayi Amfani Dashi.

Wannan Shine Hoton Da Akayi Amfani Dashi Aka Hada Dana Malam Isah Ali Pantami, Duba Da Labaran Karyar Dasuke Yawo Na Kan Cewa Akwai Soyayya Tsakaninsu.

Shafin Garkuwar Arewa A Instagram Yayi Karin Haske Akan lamarin.

garkuwanarewa BA GASKIYA BANE

Wannan hoton da ake yadawa cewa wai Maigirma Ministan Sadarwa Professor Sheikh Dr Isa AliPantami ya hadu da Hadiza Gabon ba gaskiya bane.

Hoton anyi editing ne aka hada akan application, Malam bai taba haduwa da Hadiza Gabon ba, kumabai taba kulla soyayya da Hadiza Gabon ba, layin jirgi
dabam yake da na mota.

Jama’a duk inda kuka ga wannan hoton ba gaskiya bane, sharri ne aka tsara domin a bata masa sunaMuna fatan Allah Ya tsare mana rayuwar Malam da
mutuncinsa, Allah Ya shiryar da masu masa batanci Ameen.

Wannan Shine Abunda Shafin Garkuwa Arewa Na Instagram Ya Wallafa Game Da Hoton Da Ake Yadawa Na Malam Isah Ali Pantami Da Hadiza Gabon.

Zamu So Ku Karbi Ra’ayoyinku A Sashenmu Na Tsokaci Akan Wannan Hoto Da Kuma Masu Watsa Labaran Karya, Sannan Munaso Ka Watsa Labarin Nan Domin Yaje Kunnen Mutane Dayawa Dasuke Zaton Wannan Al’amari Ya Faru, Idan Wannan Shine Karonka Na Farko A Wannan Tashar Munaso Ka Danna Alamar Kararrawa Domin Samun Sababbin Shirye-shiryenmu Akoda Yaushe mungode.

Leave a Reply

Your email address will not be published.

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

Back to top button