Tsohuwar jarumar Kannywood Mansura Isah ta bukaci gwamnatin tarayya ta samar da dokar sanya fina-fanan Hausa a kowacce jiha.

Tsohuwar jarumar Kannywood Mansura Isah ta bukaci gwamnatin tarayya ta samar da dokar sanya fina-fanan Hausa a kowacce jiha.

Jaruma Mansurah Isah ta bayyana hakane a biyo bayan yadda aka iyakance fina-finan Hausa wajen tsallakawa da su zuwa sinimomin kallo na kudancin kasar nan.

Mansurah ta bayyana hakan ta cikin wani faifen bidiyo da ta wallafa a shafinta na sada zumunta na (Instagram) a ranar Litinin din da ta gabata.

Haka zalika tsohuwar jarumar ta yi kira ga gwamnatin tarayya da ta duba yanayin dokar dake kula da sahalewar haska fina-finai a fadin kasar nan, duk da kuwa suma masu yin Hausa film sun cancanci a basu damar haska fasahar tasu a fadin kasar baki daya.

Mansurah ta ci gaba da fadin cewa “masu shirya film din Hausa suma ya kamata a kallesu tare da haska fina-finansu a ko ina acikin kasar”.

Haka kuma “na kalli yadda aka sahalewa fina-finan Nollywood, Bollywood, Hollywood nuna fina-finan dukkaninsu a fadin kasar nan sabanin na Hausa”.

“mai yasa mu Kannywood hukumar dake kula da hakan ba za ta yi wani abu akan mu, mai muka yi muku? A cewar jarumar.

“Duk da cewa muna cikin masu taimaka muku wajan harkokin zabe da sauran al’amuran siyasarku kafin da bayan kakar siyasa amma kun barmu haka”.

“Kowanne film baa bin yarwa ba ne musamman Hausa film a Najeriya, don haka ya kamata a sake duba wannan batu”.

Jarumar dai na wannan furuci ne adaidai lokacin da ta ke cigaba da bada gudunmawa a masana’antar.


Follow Hausadrop On Facebook

Leave a Reply

Your email address will not be published.

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

Back to top button