Pantami bai cancanci zama farfesa ba, In Ji Ƙungiyar ASUU

Bauchi – Kungiyar malaman jami’ar Nigeria, ASUU, reshen Jami’ar ATBU ta Bauchi ta soki nadin da aka yi wa Ministan Sadarwa da tattalin arzikin zamani, Isa Pantami a matsayin farfesa da jami’ar Tarraya ta Fasaha na Owerri, FUTO, ta yi.

Ta daga kan cewa ba a bi ka’idoji ba yayin nada shi a matsayin farfesa kamar yadda ya zo a ruwayar The Nation.

Tun bayan nada shi farfesa dai an rika cece-kuce game da lamarin.

Shugaban ATBU, Farfesa Mohammed Abdulaziz, cikin wata wasika a madadin ma’aikatan jami’ar ya taya Pantami murna kan nadin da aka masa amma ASUU ta nisanta kanta daga wasikar.

A jami’ar ta ATBU ne dai Pantami ya yi karatunsa na digirin farko ya kuma fara aiki a matsayin malami.

Jaridar The Nation ta ruwaito cewa da ya ke yi wa manema labarai jawabi a sakatariyarsu a ranar Alhamis, Shugaban ASUU na Bauchi, Dr Ibrahim Inuwa ya ce:

“Akwai matakai da ake bi kafin nada mutum a matsayin farfesa, mun gamsu cewa an bi dokokin amma duk da haka akwai alamar tambaya. Amma idan an gamsar da mu da hujoji, bamu da zabi sai dai mu amince, amma a yanzu bamu gamsu ba.

“Munyi taro a ranar 4 ga watan Nuwamba, mun amince mu nisanta kanmu daga sakon taya murnar da shugaban jami’ar ya fitar. Mun fitar da sanarwa kan hakan.”

Inuwa ya yi ikirarin cewa shugaban jami’ar bai tuntubi kungiyar ba kafin ya fitar da sakon taya murnar ga Ministan a madadinsa, ‘duba da cewa ana ta jayayya kan nadin’.

Ya kuma soki rahoton da kungiyar reshen FUTO ta fitar na wanke mahukuntar jami’ar daga saba dokoki yana mai cewa akwai ‘matsaloli da dama cikin rahoto.’

Matsayar ASUU kan batun

ASUU ta ce bayanin da ta ke da shi ya nuna cewa Ministan ya bar Nigeria zuwa Saudiya a matsayin babban lakcara.

Ya ce:

“A batun Ministan, matsayinsa na karshe a jami’ar Saudiyya shine mataimakin farfesa – wannan lakabi ne da Amurkawa ke amfani da shi. Mataimakin farfesa dai-dai ya ke da babban lakcara a kasashen da Burtaniya ta raina.”

Inuwa ya ce ka’ida shine mataimakin farfesa sai ya yi shekaru uku a matakin, ya kuma yaye dalibai na gaba da digirin farko, ya kasance cikin harkar gudanar da jami’a kuma ya zama yana yin ayyukan raya al’umma kafin ya zama farfesa.

Acewarsa, Ministan ba cika adadin shekaru ukun a makaranta ba a wannan matakin ballantana ya cancanci a nada shi farfesa.

Abin da yasa har yanzu Nigeria bata zama ƙasaitacciyar ƙasa ba, Ministan Buhari

A wani labarin daban, Ministan Kimiyya da Fasaha, Ogbonnaya Onu, ya ce har yanzu Nigeria bata cimma babban matakin da ake sa ran ta kai ba a lokacin samun ‘yanci saboda an yi watsi da irin halayen mazajen jiya da suka kafa kasar.

Ya yi wannan jawabi ne a babban birnin tarayya Abuja wurin wani taro da kungiyar ‘Yan Kabilar Igbo ta shirya don karrama Rear Admiral Godwin Kanu Ndubuisi (mai ritaya), Daily Trust ta ruwaito.

Onu ya ce ya zama dole ‘yan Nigeria su zama masu gaskiya, aiki tukuru da riko da halaye na gari idan suna son ganin kasar ta zama tauraro tsakanin sauran kasashe.


Follow Hausadrop On Facebook

Leave a Reply

Your email address will not be published.

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

Back to top button