Mun samu shakuwa da Nafisa Abdullahi a Labarina yanzu nafi jin dadin film da ita: Nuhu Abdullahi

Ashirin daga bakin mai ita da kafar yada labarai ta BBC Hausa ke yi da jaruman Kannywood sun samu zantawa da Nuhu Abdullahi Mahmud a shirin labarina inda ya amsa tambayoyi da dama a cikin shirin da suka shafi sana’ar sa da rayuwar sa.

Acikin shirin Nuhu ya sa tambayoyi kamar su tarihin sa yadda akayi ya shigo Kannywood fitowar da ya fi so a shirin labarina jaruman da yafi jin dadin fitowa a film da su da sauran su inda anan ne yake bayyana yana jin dadin fitowa da kowanne daga manyan jarumai musamman Nafisa Abdullahi da suka gina wata alaka ta sabo a shirin labarina har ya bayyana yanzu yafi jin dadin fitowa da ita a film.

Haka zalika Nuhu ya bayyana club din kwallon da yake goyon baya ya kuma bayyana wakar film din Fanan ta Umar M Shareef a matsayin wakar Kannywood da tafi burge shi a yanzu da sauran dai abubuwan da zakuji acikin shirin.

Wannan shine cikakken videon da wannan jarumi yayi bayani sosai akan rayuwarsa.

Leave a Reply

Your email address will not be published.

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

Back to top button