Nigeria Customs Service Ta Saki List Tare da Sanya Ranar Kara Bude Portal Don Yin Sabon Rijista

Hukumar Nigeria Customs Service ta saki dogon list na wadanda suka nemi aiki da  wannan hukumar a jiya Litinin. A inda kuma ta bayyana ranar da zata kara bude  portal domin sabon recruitment na shekarar 2021.

Hukumar ta sanar da cewar duk wanda yaga sunansa a wannan list daya hanzarta yin Report da kuma documentation na wadannan documents izuwa wannan office na hukumar:

“The Comptroller Establishment, Nigeria Custom Service, Old federal secretariat, Area 1 Garki Abuja daga ranar Litinin 8th November zuwa Talata 7th December 2021”

Abubuwan da za’a kai sune kamar haka:

  1. Original certificate
  2. Indigene Letter
  3. Birth certificate/Declaration of age
  4. Hotuna guda hudu (passport photographs)
  5. Photocopy guda hudu na kowane credentials

Hukumar ta kara jajjada cewar duk wanda baiyi wannan report da documentation ba a cikin wadannan kwanaki, hukumar zatayi rejecting na offer din mutum, don haka a kiyaye.

Sannan hukumar ta sanya ranar Litinin 13th zuwa ranar Friday 24th December ce ranekun da zata bude portal dinta domin daukar sabbin ma’aikatan customs a wannan official website na hukamar: www.vacancy.customs.gov.ng

Don haka duk wadanda keda sha’awar cike wannan aiki na customs sai ya shirya domin cikewa.  Hukumar na kara jan hankalin mutane dasu kula da “yan damfara masu nemar a basu kudi su bawa mutum Custom offer. Humar tace bata karbar ko kobo wajan bawa duk wanda ya can cancanta offer. Ayi hattara!

Nigeria Customs Service Shortlist


Follow Hausadrop On Facebook

Leave a Reply

Your email address will not be published.

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

Back to top button