Tsohon gwamna ya koda amaryar dansa ana tsaka da biki

Tsohon gwamnan jihar Ekiti, Ayo Fayose, ya ce dan shi da ya yi sabon aure ba shi da wata hanya da zai ci amanar amaryar shi, saboda tana da kyau da kuma kyawun sura, ga shafaffen ciki da hakori farare masu daukar hankali.

Jaridar The Cable ta ruwaito cewa wannan kalamai na tsohon gwamna an samo su ne a cikin wani bidiyon auren masoyan da yayi ta yawo a shafukan sadarwa ranar Talata, 26 ga watan Oktoba.

A cikin bidiyon, yayin da Fayose yake bayani a matsayin shi na uban ango, tsohon gwamnan ya ce kyawun mace na taimakawa matuka wajen samun daidaituwa a zaman aure.

Haka kuma ya kara da cewa mazajen da basu da mata masu kyau suna karewa wajen cin amanar matayen su.

Bayanin da ya yi cikin harshen Yarbanci, ya ce:

“Duk wanda ya ganki a yau ya san cewa nayi sa’a dana yana auren kyakkyawa. Duk wanda bashi da mace mai kyau, sai kuga ya kare wajen cin amanar matar shi. Da na bashi da wani dalili na cin amanar matar ki. Kina da kyau, ga ciki shafaffe, ga hakora farare, ga kyawun sura.”

A karshe Fayose ya yiwa ma’auratan addu’a, ya kuma shawarci dan shi da ya yi koyi da halayen shi.

Bikin auren na Oluwanigba Fayose da kuma Olamide Adekunle Abdul an gabatar da shi a wajen biki na manya dake Lekki Penninsula II, dake cikin birnin Lagos a ranar Asabar 23 ga watan Oktoba.

Ango ya fashe da kukan murna bayan amarya ta bashi kyautar dalleliyar mota a wajen daurin auren su

Wata mata ‘yar Najeriya ta yi abinda ba kasafai aka fiya yin shi a kasar ba, hakan ya sanya mutane suke ta faman tofa albarkacin bakin su akan wannan abu da tayi.

Amaryar dai ta yi abin a yaba mata, domin kuwa a ranar daurin aurensu ta fito da makullan sabuwar mota ta bawa angon nata kyauta.

A wani dan matsakaicin bidiyo da Gossip Mill Nigeria ta wallafa a shafinta, an nuno angon cikin wani yanayi na tsoro yayin da ya hango amaryar ta tinkaro shi, amma daga baya lamarin sai ya zame masa abin mamaki.

Cikin rashin sanin abinda zai faru, sai ya bata rai, inda su kuma abokanan shi suka fara tsokanar shi. Wani can daga bayan shi yana cewa wannan bai san abinda ke shirin faruwa ba.

A lokacin da ta mika masa makullin motar, bai san lokacin da ya fara kukan murna ba. Ya yi kukaa sosai saboda tsananin murna a wannan rana.

Shin kuna da wani abin cewa? za ku iya bayyana ra’ayinku a wajen sharhi dake kasa.

Leave a Reply

Your email address will not be published.

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

Back to top button