Nigeria na shirin fara qera makamai na cikin gida don tunkarar rashin tsaro da ake fama dashi.

Shugaban kasar Najeriya Muhammadu Buhari ya umarci ma’aikatar tsaron kasar ta Nigeria da ta fara sarrafa makamai na cikin gida domin cike gurbin abin da za a iya nema na makamai a daidai lokacin da kasar ke fuskantar matsalolin tsaro.

Wannan dai na zuwa ne a daidai lokacin da haramtattun makamai ke kara yawaita a hannun wadanda ba su da amincewar hukumomi wato ‘yan ta’ addan qasar, abin da ake ganin ya sa harkokin tsaro na kara tabarbarewa.

Manufar ba da umarnin ga ma’aikatar tsaro da shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya yi da ta fara kera makamai na cikin gida shi ne rage dogaro da kasashen waje wajen samun makamai da sauran kayan yaki da Najeriya ke amfani da su wajen tabbatar da tsaron kasarta.

Wannan yana nuna kenan in har an bi umarnin na shugaban kasa kamfanin sarrafa makamai wanda ke karkashin ma’aikatar tsaro ta Najeriya za ta ke samar da isassun makamai wanda ba sai an je kasashen waje an sayo su ba.

Kungiyoyin ‘yan takife da ‘yan ta’adda a Najeriya sun mallaki manya-manyan makamai

To sai ba da wannan umarni na zuwa ne a daidai lokacin da ake fama da yaduwar haramtattun makamai a hannun mutane wanda aka yi kiyasin sun wuce yawan wadanda gwamnati ta mallaka wanda kuma har ya zuwa yanzu aka kasa raba mutane da su ko ma toshe hanyoyin da ake shigowa dasu izuwa hannun mutane. 

Wannan mataki ya zo a wannan lokaci da matsalolin tsaro suka yi katutu a dukkanin sassan Najeriya. Yayin kuma da ake fargabar irin wadannan makamai za su iya fadawa hannun ba ta gari.

To sai dai masharhanta na ganin da wuya kasar ta iya samar da makamai na zamani da za a iya amfani da su wajen fuskantar matsalolin tsaro ganin yadda ‘yan ta’adda da sauran masu gwagwarmaya da makami ke amfani da manyan makamai na zamani da yanzu ma suka gagari jami’an tsaron Najeriya a wasu wuraren.

Amma wasu daga cikin talakawan kasar murna suka yi da wannan mataki saboda a cewarsu ko ba komai Najeriya za ta karu har ma wasu kasashe za su iya zuwa sayen irin wadannan makamai daga hannun Nigeria.

THANK YOU.


Follow Hausadrop On Facebook

One Comment

Leave a Reply

Your email address will not be published.

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

Back to top button