Kotun Mumbai dake india ta kama Aryan Khan dan jarumi Shah Rukh Khan da laifin mallakar miyagun kwayoyi

Kotun Mumbai dake india ta kama Aryan Khan dan jarumi Shah Rukh Khan da laifin mallakar miyagun kwayoyi

Aryan Khan wanda yake dane ga jarumin Bollywood Shah Rukh Khan, Aryan khan yana da shekaru 23 a duniya wanda wata kotu a Mumbai dake kasar india ta kamashi a cikin wani jirgin ruwa na alfarma, inda aka kamashi da miyagun kwayoyi tare da wasu mutane 7 wanda sun kasanxe abokanan sa.

Jaridar WASHINGTON D.S ta bayyaan cewa: Wata kotun Mumbai dake sakar india ta yankewa Aryan khan hukuncin zama a gidan yari na tsawon kwanaki 14.

Aryan khan an yanke masa wannan hukuncin ne sabida an kamashi da mallakar miyagun kwayoyi tare da wasu mutane 7 wanda abokanansa ne a wajan shagalin a suka shirya a cikin wani jirgin ruwa na alfarma.

A ranar asabat ne aka kama Aryan khan din da mutanen 7 alokacin da akaje kame cikin jirgin ruwan inda ake wannan shagalin a gefen gabas a tekun birnin Mumbai, a bayanin da kamfanin dillancin labaran A.P ya fitar.

Aryan khan dan jarumin Bollywood Shah Rukh Khan yan da shekaru 23 wanda kuma shine babban dan sa, a lokacin da aka kama su Aryan khan shine a tsakiyar motar ‘yan sandan.

An tsare Aryan khan ne bisa tsarin shari’a a karkashin kulawar kotu maimakon hukumar daje kula da ayyukan gyaran hali.

Jarumin Bollywood Shah Rukh Khan wanda yake da shekaru 55 yana daya daga cikin ficaccun jarumai a duniya, wanda ake masa lakabi da King of Bollywood wato sarkin Bollywood.

Shah Rukh Khan ya kwashe tsawon shekaru 30 yana shirin wasan kwaikwayo a dandalin shirya fina-finai ta Bollywood, inda Shah Rukh Khan ya fito a shirin fina-finai sama da 105.

Shah Rukh Khan yana da mabiya a shafin sa na Tweeter Miliyan 42, sannan kuma shine wanda ya mallaki kungiyar wasan kulki ta Cricket da ake kira, Knight Riders, da ake buga wasa a gasar kasar india Premier League wanda wannan wasan na Cricket yafi kowanne wasa na duniya armashi.


Follow Hausadrop On Facebook

Leave a Reply

Your email address will not be published.

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

Back to top button