Kamfanin Google na duniya zai zuba jari a yankin Africa.

Katafaren kamfanin Google wanda ya shahara kan neman bayanai a kafar zamani ta Intanet ya bayyana shirin zuba jari kimanin dalar Amirka milyan dubu (1,000,000,000.00) a nahiyar Afirka.

Kamfanin Google wanda ya yi matukar shahara kan neman bayanai a kafar zamani ta Intanet ya bayyana shirin zuba jari kimanin dalar Amirka milyan dubu a nahiyar Afirka nan da shekaru biyar masu zuwa, domin inganta hanyoyin samun intanet a nahiyar.

A ciki kamfani zai saka waya ta karkashin teku domin hada nahiyar da sabbin hanyoyin sadarwa na zamani inda wayar zai ratsa cikin qasan teku zuwa kasashen Turai ta karkashin tekun.

Sundar Pichai babban jami’in kamfanin na Google ya bayyana haka, inda ya ce wayar ta karkashin kasa za ta ratsa kasashen Afirka ta Kudu, da Nambiya gami da Najeriya zuwa tsibirin St Helena wanda yake gefen kasar Afirka ta Kudu wanda kuma har yanzu yake karkashin mulkin mallaka na Birtaniya.

Sannan kamfanin na Google zai samar da bashi mai sauki biya na dalar Amirka milyan goma (10,000,000.00) ga masu kananan sana’o’i na da masu kirkiro ayyuka a kasashen Ghana, da Kenya, da Najeriya gami da Afirka ta Kudu, domin rage radadin da aka fuskanta sakamakon annobar cutar coronavirus (COVID-19) da duniya ta fuskanta daga shekarar 2019 har ila yau.

THANK YOU FOR VISITING OUR SITE. #hausadrop

Leave a Reply

Your email address will not be published.

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

Back to top button