Shugaban kasa Muhammad buhari ya gabatar da Kasafin kudin 2022: Naira trillion 16 ya ce za a kammala ayyukan da aka soma.

A zaman da aka gabatar dashi a yau cikin majalisar tarayya ta kasa (Nigeria) Shugaban qasar Muhammadu buhari ya ce kasafin kudin na sabuwar shekara me kamawa 2022, zai mayar da hankali ne kawai wajen kammala dukkanin wasu ayyukan da gwamnatinsa ta soma kuma qudurin kasafin kuɗin sabuwar shekarar me kamawa na 2022, wanda ya kai kimanin naira tiriliyan goma sha shida 16 da ɗigo 39. (16.39 trillions naira)”

Kuɗin dai, ƙari ne a kan naira tiriliyan 13.98 na kasafin kuɗin shekarar 2021.

Gwamnatin shugaban kasar ta bayyana shirinta na ciyo qarin bashi don samun karin kudi har Naira tiliyan 6 da biliyan 258, da zata cike gibin da za a samu a kasafin kudin da shugaban zai gabatar na shekarar 2022.

Daga cikin kudin da shugaban kasar ya gabatar a kasafin kudin na 2022, har da muhimman bangarorin da za’a warewa kudade kamar hukumar zaben kasar wato INEC wadda ake sa ran tanadar mata karin naira biliyan 100, don shirin kasar na tunkarar babban zaben 2023 da za’a gabatar.

A yayin gabatar da kasafin kudin dai, shugaban na Najeriya ya sanar da ajiye gangar man fetir daya a kan farashin dala $57, da kuma hako man fetir ganga kusan miliyan biyu a kullum.

Sai kuma canjin dala daya a kan Naira 410 da silai 15 (410.15) da kuma hasashen samun kudin shiga Naira tiriliyan 3 da digo 15 daga bangaren man fetur.

Inji Ahmad Lawan shugaban majalisar dattawan Najeriya yace “Za mu amince da kasafin a cikin wannan shekarar”

Senate Ahmad Lawan of Nigeria

Shugaban majalisar dattawan Najeriya, Ahmad Lawan ya ce majalisar dokoki za ta amince da kasafin kudin 2022 kafin karshen wannan shekarar.

Ahmad Lawan ya bayyana haka ne a jawabinsa na maraba kafin shugaba Buhari ya gabatar da kasafin kudin 2022 a zauren majalisar dokokin kasar.

Bayan godewa shugaban kasa Muhammadu Buhari, shugaban majalisar dattawan ya ce ‘yan majalisar za su yi aiki ne tuquru domin ganin an soma aiki da sabon kasafin kudin a cikin sabuwar shekara 2022.

By hausadrop.com


Follow Hausadrop On Facebook

Leave a Reply

Your email address will not be published.

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

Back to top button