Yadda zaku sani idan an amince daku karbi bashin NIRSAL COVID-19 2021.

Yawancin mutane masu neman a basu loan ma’ana rancen kudi da federal government take bayarwa basusan taqamaimai me ake nufi da kalmar loan ba. Suna shiga ciki ne kai tsaye kawai saboda su kudin suke hanga.

Yakamata mutane su lura da jumla ta gaba wato maganar da xata biyo baya.

Lamunin ba kyauta bane!! za a biya shi cikin shekara uku ne ko kuma shekara biyu, ya danganta dai da tsawon lokacin da mutum ya cike a lokacin da yake neman wannan bashin, amma dai qarshen lokacin da zaka dauka baka biya wannan kudin ba shine shekara uku. Tunda an riga har an haɗa BVN ɗinka zuwa asusunka na banki, to babu wata hanya da za ku iya tserewa biyan bashin idan har lokacin yayi. Dazarar lokacin daka dauka yayi kuma baka biya ba to indai har akwai kudi a cikin asusunka na banki to kawai zasu dauki kudinsu ne ba tare dasun sanar maka da xasu dauka ba.

Don sanin idan har yanzu kuna kan hanya, ci gaba da duba matsayin ku akan portal dinsu. Kuna iya neman rancen, amma bai zama lalle za ku samu nan da nan ba.

Dole ne ku sami bayanin martaba wato profile tare da platform din don sauƙaƙe bin diddigin matsayin ku. Idan ba ku dashi, to ƙirƙirar sabon profile ya kamaku tare da su.

Ya kamata ku lura da cewa samun bayanin martaba wato profile tare da su wannan portal din na NIRSAL baya bada garantin cewa zaku sami rancen wannan kudin. Akwai ƙa’idodi waɗanda za su buqaci da idan har kun cancanci dasu bakun to tabbas babu makawa zasu baku wannan rancen.

Shin ko kuna da adireshin imel mai inganci?

Wannan tambaya ce kawai, amma tana da matukar muhimmanci. Saboda ta hanyar ne za’a sanar da ku daga portal din in harsun amince dasu baku wannan kudin.

Amma dai hanya mafi inganci dasukafi sanarwa da mutane sun aminta dasu baka wannan kudin shine ta hanyar turo maka da saqo ta kan layin wayarka wanda ka cike profile din dasu.

Akwai nau’ikan lamuni guda biyu akan portal din. Ku kula da su don gujewa rudani yayin aiwatarwa.

Sannan daga wannan matakin zasu nemi ku samar da BVN dinku.

Sun san mahimmancin BVN ɗin ku, don haka za su buƙace shi. Idan kun wuce matakin tabbatar da BVN, to zaku iya zaɓar adadin kudin da kukeso su baku.

Bayan haka, kuna buƙatar daku cika bayanan asusun ku daidai ba tare da samun wata matsala ba. Ba za’a ɗora alhakin akansu ba idan kun rasa wannan matakin. Kuna buƙatar yin taka tsantsan a nan sosaii.

Mataki na ƙarshe shine yarda da sharuɗɗan su. Idan kuna shakkar sharudan nasu, to ku koma baya ku karanta ta hanyoyin. Zai nuna muku abin da kuke buƙatar sani da yadda yakamata ku biya bashin.

MUNGODE DA KASANCEWARKU TARE DA HAUSADROP.

Leave a Reply

Your email address will not be published.

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

Back to top button