Maharan ‘yan bindiga sun kai mummunan hari jihar Zamfara inda suka kone gidaje da motoci

Maharan 'yan bindiga sun kai mummunan hari jihar Zamfara inda suka kone gidaje da motoci

‘Yan bindiga sun kai hari kauyen kuryar Madaro a karamar hukumar kauran Namoda a jihar Zamfara, a rahoton da BBC Hausa suka samu sun bayyana cewa, ‘yan bindigar sun hallaka mutane da dama sannan kuma sun kone gidajen mutane tare da motoci.

Wasu al’ummar da suke yankin sun tabbatar da cewa: Maharan sun shiga kauyen ne da misalin karfe 10:00 na dare, inda sukaci karansu ba babbaka a kauyen, sannan ‘yan bindigar sun debi kayayyakin abinci na ‘yan kasuwar yankin tare da sace dabbobin mutane.

Rundunar ‘yan sandan jihar Zamfara sun tabbatar da harin da aka kai kauyen, amma tuni aka tura jami’an tsaro kauyen domin akai dauki, kauyen da maharan suka kai harin yana daya daga cikin yankunan da hukumomin jihar suka dauki matakin bakile sabis da kuma intanet.

Sai dai kuma wasu mutanen kauyen wanda suka tsere suka koma Gusau inda aka dage musu dokar hana amfani da sabis, sun bayyana cewa ‘yan bindigar sun kona gidaje kusan 13 da kuma motoci 16.

Wasu hotunan da suka bayyana sun nuna yadda aka kone gudajen da kuma motocin a harin da aka kai, hakan yazo ne bayan hukumar jihar ta dauki tsauraran matakai domin magance ta’addancin da ‘yan bindigar suke a jihar ta Zamfara.

Ga hotunan da maharan ‘yan bindigar suka kone gidaje da motocin nan a kasa sai ku kalla.


Follow Hausadrop On Facebook

Leave a Reply

Your email address will not be published.

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

Back to top button