Kalli hotunan tsohuwar jarumar kannywood Wasila tare da mijinta suna murnar cika shekaru 19 da aure su

Kalli hotunan tsohuwar jarumar kannywood Wasila tare da mijinta suna murnar cika shekaru 19 da aure su

Tsohuwar jarumar kannywood Wasila jaruma ce wanda ita ma ta taka rawar gani a masana’antar ta kannywood lokacin da take sharafinta, a sanda akayi shirin fim din Wasila da ita wanda jarumi Ali Nuhu ya fito a matsayin mijinta.

Fim din Wasila yayi daukaka sosai a masana’antar ta kannywood har ma a wajan al’umma masu kallo wanda ya sami karbuwa a wajan jama’a sabida fim din ya tsaru.

Sai a yau ne jarumar ta wallafa hotunan su da ita da mijinta tare da ‘yayan su 4 suna murnar cika shekaru 19 da auren nasu, Wasila Isma’il da mijin nata Al’amin a yau ne suka murnar cika shekaru 19 da auren nasu wanda Allah ya albarkace su da haifar ‘yar ‘yar 4 mata 3 namiji 1, wanda zaku gani a cikin hotunan dake kasa.

Muna rokon Allah ya kara abarka kan aure nasu ya karo musu zuri’a ta gari dayyaba.

Ga hotunan a kasa domin kun kalla.

Leave a Reply

Your email address will not be published.

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

Back to top button