Da dumi-dumi: Shugaba Buhari ya yi ganawar sirri da Goodluck Jonathan

Jaridar Daily Trust ta ce, shugaban kasa Muhammadu Buhari a ranar Laraba 6 ga watan Oktoba ya yi wata ganawar sirri da tsohon shugaban kasa, Dakta Goodluck Jonathan, a fadar shugaban kasa da ke Abuja.

Legit.ng ta tattaro cewa ba a san dalilin ziyarar ba saboda Jonathan bai yi magana da manema labarai ba bayan taron.

Da dumi-dumi Shugaba Buhari ya yi ganawar sirri da Goodluck Jonathan
Image Source: Legit Hausa

Sai dai kuma, an lura cewa tsohon shugaban, a matsayinsa na wakilin ECOWAS na musamman a Mali, yana ta yin taro akai-akai tare da Shugaba Buhari kan kasar ta Yammacin Afirka da ke fama da rikici.

Akwai kuma rade-radin cewa wasu jiga-jigan jam’iyyar APC mai mulkin kasar suna zawarcin Jonathan da tikitin takarar shugaban kasa na 2023.

Source: Legit Hausa

Leave a Reply

Your email address will not be published.

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

Back to top button