HUKUMAR N-POWER TA KAMMALA SHIRIN BIYAN BASHIKAN N150,000 BATCH A DA B NA 2016/2018

Hukumar nan dake kula da shirin N-Power wato Federal Ministry of Humanitarian Affairs, Disaster Management and Social Development tace ta kammala shirin biyan dukkan bashikan da ake bin hukumar tun daga shekarar 2016 zuwa 2018 na Batch A da B.

Hukumar ta ware accounts guda 14,021 wadanda ta fara biyansu tun daga March 2020 a karkashin shirin nan na gwamnatin tarayya, GIFMIS (the government Integrated Financial Management Information System) a inda hukumar kawo yanzu ta tantance accounts guda 9066 wadanda hukumar ta fara biyansu kudadensu. Hukumar ta kara da cewar ta fuskanci tarin matsaloli ne a sakamakon wadannan matsaloli kamar haka:

1.        Daliban da keda accounts da yawa (beneficiary having multiple accounts)

2.        Da kuma beneficiaries dake karbar albashi a gwamnati ko kuma wata wata ma’aikata mai zaman kanta. Hakan ya sabawa sharudodi da ka’aidojin da hukumar ta shinfida

Hukumar tace ta aiwatar da cikakken bincike gameda yadda ta fitar da beneficiaries guda 9066 wadanda zata bawa kowannensu N150, 000.00 a account dinsa. Hukumar tace tana kan cigaba da bincike kan ragowar beneficiaries guda 4955 wadanda basa cikin wadanda zasu sami wannan payment.

Hukumar na kara kokwantawa da irin jinkirin da takeyi amma tana kara bawa al’umma kwarin gwiwar cewar zatayi iyaka bakin kokarinta wajan ganin komi ya tafi dai dai.

Leave a Reply

Your email address will not be published.

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

Back to top button