Bayani Akan Jinin Haila ko Jinin Al’ada Asaukake Kashi Na Uku

Da sunan Allah mai rahma mai jinkai, Allah kayi salati da salami ga mai garin Madina.

Related Articles

Bayani Akan Jinin Haila ko Jinin Al'ada Asaukake.

KASHI NA’UKU

IDAN JINI YAI WASA

Misali mace tanayin haila duk wata kwana uku, Amma wani watan batayi ukun ajereba,

Misali:- tayi haila ranar juma’a sai batayi ranar asabarba,sai tayi ranar lahadi, batayi ranar litininba,sai tayi ranar talata, to sai tahada lissafi,sai tace,ranar juma’a daya,sai ta tsallake asabar tunda batayi ba,sai tace lahadi biyu, sai ta tsallake litinin, sai tace talata uku, Haka ko da yana tsallaken kwanakine haka za tayi lissafi banda kwanakin da batayi ba Kwanakin da taga jini shi zata lissafa.

Amma idan taga jini yau sai ya dauke bata sake ganiba sai bayan kwana takwas to jini na biyu ya zama sabuwar haila.


Amma wasu malamai sunce sai yakai kwana shabiyar yazama sabuwar haila, Amma in taga jini yau sai ya dauke sai bayan kwana shabiyar ta sake gani to ya zama wannan jinin sabuwar hailace, wannan maganar ita tafi karfi.

Haka idan mace tayi kwanakin da tasabayi kuma jini bai tsayaba, To sai takara kwana uku idan bai tsayaba bazata karaba a wannan watan, sai tayi wanka tayi sallah.

Bawai zatayi ta kara uku uku bane har kwana shabiyar, A a inta kara ukun a wannan watan shikenan, saidai bayan karin da tayi a wannan watan in wani watan yazo shine zata kuma kara ukun a haka zata dinga kari har zuwa kwana goma shabiyar.

Sai an lura dan wannan yanada rikici ga masu haila, Allah ya fahimtar damu albarkar manzan Allah.

Muhadu a kashi na hudu In Allah ya yarda.

ABU MADINA
ALI AUWAL ZAGE

Dan Karin Bayani: 08067238367

Leave a Reply

Your email address will not be published.

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

Back to top button