Ɓatanci: Dalilin da yasa na goge sukar da nayi kan kisan Deborah, Atiku Abubakar

Tsohon mataimakin shugaban ƙasan Najeriya, Atiku Abubakar, ya bayyana dalilin da ya sanya ya goge rubutun da yayi kan kisan da akayi wa ɗalibar nan Deborah, wacce aka zarga da yin ɓatanci ga annabi Muhammad (SAW).

Atiku Abubakar ya bayyana yadda yake tafiyar da lamarin shafukan sa

Jaridar Premium Times ta rahoto cewa Atiku Abubakar wnda yayi magana a ranar Juma’ah, ya bayyana cewa duk wani rubutu a shafukan sa na sada zumunta sai sun sami yarjewar sa kafin a wallafa su.

Atiku Abubakar wanda yana ɗaya daga cikin ‘yan takarar shugaban ƙasa a ƙarƙashin inuwar jam’iyyar PDP, ya faɗi hakan ne a yayin da ya kai ziyarar neman shawara ga gwamnan jihar Edo, Godwin Obaseki, a gidan gwamnatin jihar da ke Benin.

Tun da farko Atiku Abubakar yayi magana akan kisan da aka yiwa Deborah Samuel wacce ake zargin yin ɓatanci ga annabi (SAW).

Sai dai ya goge rubutun na sa, wanda hakan ya janyo masa suka sosai a kafafen sada zumunta.

Ya bayyana dalilin goge rubutun

Atiku Abubakar ya bayyana cewa:

Duk wani rubutu a shafuka na, sai ya samu amincewa ta, amma wannan bai samu ba, saboda haka na sanya su goge shi.

Na ɗauki matsaya akan Shari’ar musulunci, kuma an zage ni, an jefa min duwatsu, amma zuwa yaushe aka daina? Duk da hakan ban sauya matsaya ta akan hakan ba. Ba na jin tsoron ɗaukar matsaya akan lamurra masu muhimmanci.

Source: Labarun Hausa

Leave a Reply

Your email address will not be published.

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

Back to top button